Lompat ke konten Lompat ke sidebar Lompat ke footer

Gwamna a Arewa Ya Taso Masu Zanga Zanga a Gaba, Ya Yi Kakkausan Kashedi

  • Gwamnatin Kaduna ta gargaɗi matasa cewa ba za ta lamunci duk wata zanga zanga ba tare da izinin hukumomin tsaro ba
  • Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya ce sun gano wasu miyagu da ke shirin fakewa da zanga zanga su tayar da fitina a Kaduna
  • Aruwan ya ce daga yanzu gwamnati ta haramta duk wani gangami da bai samu sahalewar jami’an tsaro ba a faɗin jihar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al’amuran yau da kullum

Kaduna – Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wata zanga-zangar da hukumomin tsaro ba su amince da ita ba.

Gwamnatin karkashin Malam Uba Sani ta ce ɓata gari na amfani da irin wannan zanga-zangar wajen wawushe dukiyar gwamnati da ta al’umma, don haka ta taka ma abin burki.

Kara karanta wannan

An gano mutane 19 da suka mutu sakamakon mummunan haɗarin jirgi

Malam Uba Sani.
Gwamna Uba Sani ya haramta zanga zangar da babu amincewar jami’an tsaro a Kaduna
Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kaduna ta gindaya sharaɗi

Ya ce gwamnatin Kaduna ba za ta sake lamuntar mummunan lamarin da ya auku a ranar 1 ga watan Agsuta, ranar da aka fara zanga-zanga ya kara faruwa ba.

Aruwan ya ce munanan abubuwan da suka faru a ranakun 1 da 5 ga watan Agusta alamu ne karara da ke nuna miyagu na kulla yadda za su angiza Kaduna cikin tashin hankali.

“Gwamnatin Kaduna da jami’an tsaro ba za su tsaya suna kallo masu manufar ruguza jihar su cimma nasara ba tare da ɗaukar mataki ba.

“Muna ƙara kashedi da babbar murya cewa ba za mu bar duk wasu miyagu da ke fakewa da sunan zanga zanga su tayar mana da tarzoma ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Sojojin Najeriya sun yi magana kan kifar da gwamnatin Bola Tinubu

– Samuel Aruwan.

Abin da doka ta tanada kan zanga-zanga

Kwamishinan ya ƙara da cewa duk da mutane na da ya halatta mutane su yi zanga-zanga a dokar ƙasa, amma haram ne yin duk wani gangami da tare da sahalewar hukumomin tsaro ba.

Matasa sun fito zanga-zanga a Abuja

Kun ji cewa masu zanga zanga sun sake tururuwa a kan tituna a babban birnin tarayya Abuja yau Asabar, 10 ga watan Agusta, 2024.

Tuni dai ƴan sanda suka ƙara tsaurara tsaro a kwaryar birni tun ranar Jumu’a saboda masu zanga-zanga na shirin rufewa da gagarumin tattaki.

Asali: Legit.ng




,

Posting Komentar untuk "Gwamna a Arewa Ya Taso Masu Zanga Zanga a Gaba, Ya Yi Kakkausan Kashedi"